11 Oktoba 2024 - 11:00
Bidiyon Yadda Makamai Masu Linzami Na Hezbollah Suka Isa Birnin Kiryat Bialik Na Isra'ila

Hizbullah ta kai hari a birnin Kiryat Bialik da ke arewacin yankunan da aka mamaye.

                 Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA - ya kawo maku rahoto daga majiyoyin yada labaran cewa sun ba da rahoton kan harin roka da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kai kan birnin Kiryat Bialik da ke arewacin yankunan da ta mamaye. Birnin Kiryat Bialik yana tsakanin garuruwan Haifa da Acre inda kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta harba makamai masu linzami zuwa wannan birnin tare da kuma sun kai ga inda aka harba su.

Harin makami mai linzami da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kai kan birnin Kiryat Bialik ya haifar da barna mai yawa a daya daga cikin masana'antun wannan birni na sahyoniyawan.


Birnin Kiryat Bialik yana a arewacin birnin Haifa, a arewacin yankunan da aka mamaye, kuma wannan birni yana da kusan 'yan sahayoniya dubu 36.

A cikin 'yan kwanakin nan da makwannin da suka gabata, birnin Kiryat Bialik na yahudawan sahyuniya yana shan fama da hare-haren rokoki na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, lamarin da ya yi illoli da cikas na gudanuwar rayuwa a wannan birni.