8 Oktoba 2024 - 18:39
Mayakan Hizbullah Na Kasar Labanon Sun Tilastawa Sojojin Yahudawan Sahyoniya Gudu A Yankin Kan Iyaka + Hotuna

Majiyar kasar Labanon ta rawaito cewa wasu gungun sojojin yahudawan sahyoniya sun shirya kai farmaki kan yankunan kasar Lebanon da yammacin yau domin su isa bayan shelkwatar UNIFIL.

Bayan lura da tantance wadannan sojoji, dakarun Hizbullah sun kai musu hari da kazamin hare-haren rokoki, sannan kuma da dama daga cikin mayakan wannan yunkuri sun yi artabu da su kai tsaye.

Majiyoyin na Lebanon sun ce a yayin wannan rikici an kashe sojojin Isra'ila da dama tare da jikkata wasu da dama, yayin da sauran mutanen da suka rage aka tilasta musu juyawa da baya zuwa yankunan da aka mamaye.

Mayakan Hizbullah na kasar Labanon sun tilastawa sojojin yahudawan sahyoniya gudu a yankin kan iyaka

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da yin arangama da mayakanta da wani bangare na sojojin yahudawan sahyoniya a yankin Al-Labuna da ke kan iyakar kasar, lamarin da ya kai ga tserewar sojojin yahudawa daga wannan bangare kuma a cewar sanarwar kungiyar Hizbullah ta tabbatar da samuwar hasarar rayuka na sojojin gwamnatin mamaya.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul Bait (AS) – ABNA- ya nakalto maku daga Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran shi ma ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Ahed cewa, kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa mayakanta sun tilastawa wani bangare na sojojin yahudawan sahyoniya gudu a yankin Al-Labuna da ke kan iyaka.

Bayanin na Hizbullah ya ci gaba da cewa: A ci gaba da goyon bayan al'ummar Palastinu masu gwagwarmaya a zirin Gaza da jarumtaka da gwagwarmayar da suke da shi, da kuma kare kasar Labanon da al'ummarta, da misalin karfe 2:00 na safiyar yau Talata 8/10/2024 ne wani gungun sojojin yahudawan sahyoniyawan a yayin da suke son kutsawa kan iyakar Al-Labuna suna masu garuwa da buldoza da motocin soji, mayakan Islama sun yi musu ruwan harsasai da rokoki, lamarin da ya yi sanadin jikkatar wasu daga cikinsu tare da tilasta musu ja da baya.

Tun da farko Al-Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, an yi artabu kai tsaye tsakanin dakarun gwagwarmaya da kuma wasu gungun dakarun yahudawan sahyoniya da suka kutsa daga bayan hedkwatar UNIFIL.

A cewar wannan rahoto, Mujahidan sun dauki matakin tinkarar wannan dakarun yahudawan sahyoniya da mamaki inda suka far musu a wani harin kwantan bauna da suka yi, wanda hakan ya janyo hasarar rayuka na makiyan.

Kamfanin dillancin labaran Al-Mayadeen ya bayar da rahoton cewa, babban farmakin da dakarun gwagwarmaya suka kai ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama daga cikin sojojin na musamman na haramtacciyar kasar Isra'ila a yankin Al-Lubuna.

A baya dai wani kwamandan na kungiyar Hizbullah ya ba da labari game da yunkurin shakku na sojojin yahudawan sahyoniya a kudancin kasar Labanon da kuma yuwuwar sojojin mamaya su shiga karkashin rundunar UNIFIL (dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke Lebanon).

"Stefan Dujarric" mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya a yayin da yake nuna damuwa game da yunkurin dakarun yahudawan sahyoniya ya bayyana cewa: UNIFIL ta bayyana matukar damuwarta game da yunkurin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi a baya-bayan nan a kusa da daya daga cikin wuraren da dakarunta da aka ambata.

Dujarric ya kara da cewa: Ba za’a yarda da cutar da jami'an tsaron da ke da alaka da Majalisar Dinkin Duniya, wadanda ke aiki da kuma aiki bisa umarnin kwamitin sulhu na MDD.