Rundunar sojin Isra'ila ta sanar
da cewa, an aike da runduna ta uku (91st) da ta kunshi runduna ta 3 zuwa
kudancin kasar Lebanon domin taimakawa sojojin bangarorin biyu da suka gabata
wadanda suka yi asara mai yawa a cikin makon jiya.
Fitattun sojoji na sojojin Sahayoniya sun tabbatar da cewa: Ba za mu iya zama a Gaza har abada ba/Hamas na da makamai da yawan gaske.
Fitattun sojojin yahudawan sahyoniya a ranar tunawa da harin guguwar Al-Aqsa: qudire-quderen da tsare-tsaren da hukumar Isr’aila ta yanke a matakan siyasa dangane da yakin ba su da wani amfani.
Muna ganin mummunan sakamakon yaki da tattalin arziki, rayuwa da ci gaba da daukar aikin soja, da kuma koma bayan iko.
Sojojin yahudawan sahyoniya a cikin wata sanarwa sun amince da cewa: an samu mutuwar sahyoniyawa 726 da kuma harba dubun dubatan rokoki kan gwamnatin sahyoniyawa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, sojojin gwamnatin yahudawan sahyoniya sun tabbatar da mutuwar sahyoniyawa 726 tare da harba dubun-dubatar makaman roka a yankunan da aka mamaye daga fagagen Lebanon, Gaza da Iran cikin shekara guda.
Duk da Ana buga wadannan kididdigar asarar rayuka ne yayin da gwamnatin sahyoniyawan ke hana buga sahihin kuma cikakkun labarai na kididdigar asarar da gwamnatin Sahayoniyya ta yi tare da yin katsalandan a kafafen yada labarai.
Yanzu yanzu kafi hada wannan rahohon an Harba wasu rokoki 20 zuwa ga Al-Jalil
Kamar yadda Tashar talabijin ta 12 ta gwamnatin Sahayoniya ta sanar da cewa an harba makaman roka guda 20 daga kasar Labanon zuwa Galili Alya da ke arewacin Palastinu da aka mamaye.
Majiyar masu magana da harshen yahudanci sun jaddada cewa a sakamakon wannan harin motoci da dama sun kama da wuta tare da yin barna mai yawa a wasu garuruwa da suka hada da Tarshiha da Kafardim.