Majiyoyin Labarai yahudawa masu magana da harshen yahudanci sun sanar da cewa a cikin sa'o'i da suka gabata an jikkata sojojin Isra'ila 47 a fagagen yaki daban-daban a kudanci da arewacin Palastinu da aka mamaye, kuma yanayin 5 daga cikinsu na da matukar tsamari.
Hezbollah tabbatar da cewa ta jefa bama-bamai da makamai masu linzami a wurin taron gungun sojojin makiya Isra'ila a yankin Jal al-Deir wanda Hukumar Yada Labarai ta Isra'ila ta tabbatar da cewa Kimanin kashi ɗaya bisa huɗu na Isra'ilawa sun ce sun yi tunanin barin ƙasar a cikin shekarar da ta gabata saboda rashin tabbacin tsaro wannan na biyowa bayan hare-haren da gwagwarmaya ke kaiwa Isra'ila.
A yanzu yanzu kuma Gidan labaran yanar gizo na Walla ya hakaito cewa asibitin Ziv da ke Safed yana dauke da mutane 110 da suka samu raunuka sun, ciki har da sojoji, sakamakon ta'azzarar wutar roka, da kuma jiragen yaki marasa matuki a 'yan kwanakin nan.