Cikakkun bayanai kan mummunan harin kwantan bauna da dakarun kasar Labanon suka yi wa dakarun yahudawan sahyoniya kamar yadda Kamfanin dillancin labaran tashar Aljazeera ta kasar Qatar ya kawo cewa, sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suna kan iyakar kasar Lebanon da Palastinu suna wuta daga kungiyar Hizbullah, kuma sojojin na yaƙi da wadannan mayakan da makaman da suka dace.
Fuskantar makiya yahudawan sahyoniya bai takaitu ga abubuwan da suka kutsa cikin kasar Labanon kadai ba, har ma da bangaren sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke cikin yankunan Falasdinawa da suke mamaye da su, su ne wuraren da kungiyar Hizbullah ke ci gaba da kaiwa hari.
An kashe fitattun sojoji da masu kula da sojojin makiya yahudawan sahyoniyawan da suka shiga cikin kasar Lebanon ko dai an kashe su ko kuma suka jikkata ko kuma sun gudu.
Jarumtar da dakarun Hizbullah suka haifar a jiya Laraba a kudancin kasar Lebanon ya yi sanadin mutuwar sojojin yahudawan sahyoniya sama da 80 tare da jikkata wasu tare da tarwatsa tankokin yaki na sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila 5.
A safiyar jiya Laraba ɗin dai wasu gungun jami’an sojin Isra’ila su 30 ne suka shiga yankin tare da fadawa tarkon ‘yan kwanton baunar suka makale a wurin.
Hakan fa duk yana zuwa ne bayan da Isra'ila ta gargadi sojojinta akan suyi takatsantsan fa su yi hattara kar masu tsaro na Hizbullah su yi garkuwa da su ko su fada tarkonsu.
A yammacin jiya Laraba tashar "Al-Mayadeen" ta nakalto daga tashar talabijin ta 13 ta gwamnatin sahyoniyawa ta bayar da rahoton cewa, sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun nemi sojojinsu da su yi taka tsantsan don kada jami'an tsaron sashen Ridwan na Hizbullah su yi garkuwa da su bayan shiga kasar Lebanon.
Dakarun Ridwan wani bangare ne na kwararrun mayaka na kungiyar gwagwarmaya Hizbullah ta kasar Labanon, wadda wannan sashen dakarun ne suka jagoranci wannan abun da ya faru a jiya ga sojojin Yahudawa.