Kamar yadda tashar labarai ta -IRNA- ta fitar cewa Sojojin yahudawan sahyoniya sun sanar da kutsawar jiragen yaki marasa matuka guda biyar cikin birnin Tel Aviv.
A cewar rahoton da kafar yada ta IRNA ta samo daga kafofin labarai na Falasdinawa da suka fitar a safiyar Alhamis din nan, na'urar jami'an tsaron yahudawan sun yi nasarar harbo wani jirgin mara matuki daga cikin jiragen biyar ɗin.
Yahudawan sahyoniya da dama ne suka jikkata yayin da suke gudun tsira da rayuwarsu zuwa mafaka, sannan an aike da jami'an agajin gaggawa na gwamnatin sahyoniyawan zuwa "Bat Yam" da ke kudancin birnin Tel Aviv domin kula da wadanda suka jikkata.
Kafofin yada labaran gwamnatin yahudawan sahyoniya sun kuma bayar da rahoton an samu wasu kutsen jiragen yaki marasa matuka a yankin Golan da aka mamaye.
Wasu kafafen yada labarai sun bayar da rahoton cewa an kunna siren na kararrawa a yankin Golan da aka mamaye bayan gazawar tsaron sararin sama wajen tunkarar jiragen.
