Mayakan Hizbullah sun lalata tankokin yaki guda uku na gwamnatin
sahyoniyawa.
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (As) - ABNA- ya habarto maku cewa: kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da sanarwar lalata tankokin yaki guda uku na gwamnatin sahyoniyawa a kudancin kasar Labanon.
A cewar sanarwar da wannan kungiyar gwagwarmaya ta yi, an lalata tankokin yaki guda uku na gwamnatin sahyoniyawa sakamakon harba makami mai linzami da mayakan Hizbullah suka yi a sa'o'i guda da suka gabata a lokacin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai ga garin Maron al-Ras da ke kudancin kasar Labanon.
Kafofin yada labaran yahudawan a baya sun tabbatar da cewa an kashe sojoji takwas na gwamnatin sahyoniyawan a wani artabu da mayakan Hizbullah a kudancin kasar Lebanon.
A safiyar ranar Talata 01 ga watan Oktoban shekarar 2024 ne sojojin kasar Isra'ila suka sanar da fara kai farmaki ta kasa a kudancin kasar Lebanon kan mayakan Hizbullah na kasar Labanon.
Kafofin yada labaran yahudawan sahyoniya sun tabbatar da cewa An kai masu wani gagarumin kisan kiyashi a kudancin kasar Lebanon inda dukkan mutanen da ke cikin tankunan suka kone.
Kafafen yada labaran yahudawan sahyoniya sun bayyana harin da kungiyar Hizbullah ta kai wa tankunan yaki da dakarunta a arewacin yankunan da aka mamaye a matsayin wani lamari mai matukar wahala da tsaro.
Bisa rahoton tashar Al-Mayadeen yazo cewa, a wannan harin, an kona dukkanin tankunan yaki 3 na sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila tare da kashe sojojin da ke cikin tankunan.
Rahotanni sun bayyana cewa, an shafe sa'o'i kadan da suka gabata ana kazamin rikici a yankunan Yaroun da Maroun al-Ras da ke kudancin kasar Lebanon.
Har ila yau dakarun na Hizbullah sun tayar da wani bam a kan hanyar da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka bi, inda suka kashe sojojin Isra'ila da dama tare da jikkata wasu da dama.
Kafofin yada labarai na Ibraniyawa sun ce game da kisan da aka yi wa dakarunsu: An yi wa sojojinmu kisan gilla a kudancin Lebanon.
...................................


