Kungiyar Hizbullah ta kasar
Labanon ta sanar a yau Laraba cewa: Mayakan gwagwarmayar Islama na kasar
Labanon suna fafatawa da sojojin yahudawan sahyoniyawan da suka kutsa kai garin
Maroon al-Ras da ke kan iyakar kasar ta Lebanon daga gabas.
Kungiyar Hizbullah ta kara da cewa: A cikin wannan rikici an raunata dimbin sojojin yahudawan sahyoniya kuma har yanzu ana ci gaba da gwabzawa.