2 Oktoba 2024 - 08:17
Sama Da Yahudawan Sahyoniya 20 Ne Aka Kashe Da Raunata Wasu A Harin Kwanton Bauna Na Hizbullah

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da cewa ta kai hari kan taron sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila a barikin Shamira tare da kashe wasu daga cikin wadannan mutane tare da jikkata wasu.

Har ila yau, an bayar da rahoton cewa, an samu nasarar harin da dakarun Hizbullah na kwanton bauna a garin Al-Adisah inda harin ya hada sosjojin Komando 20, inda aka aike da jirage masu saukar ungulu 4 na Isra'ila domin jigilar wadanda suka jikkata da kuma wadanda suka mutu.

 Kafofin yada labaran yahudawan sahyuniya sun tabbatar da cewa an kashe sojoji 4 tare da raunata 20 a harin kwantan bauna da kungiyar Hizbullah ta kai a garin Al-Adisa.

 Mutane 15 ne suka mutu da jikkatar wasu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai kan Sahayoniyawa Sojojin Isra'ila da suka ji rauni ya tsananta a harbin Tel Aviv

Akalla yahudawan sahyuniya 7 ne suka mutu inda wasu 8 suka samu raunuka sakamakon harbin da aka kai a birnin Jaffa na Tel Aviv wanda bai samu kulawa da daukar hankali ba sosai ba sakamakon harin na Iran mai Taken Tabbatacen Alkawari Na 2.

A cewar rahotanni da aka buga, mutane biyu daya dauke da makami daya kuma dauke da wuka, sun kai wani samame a Tel Aviv.

Sojojin yahudawan sahyoniya sun tabbbatar da cewa wata mace sojan sahyoniyawan ta samu munanan raunuka a wannan farmakin kuma halin da take ciki na cikin mawuyacin hali.