Kamar yadda Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, a cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fitar ta bayyana cewa, ta kai hari da makami mai linzami da dama a sansanin sojojin makiya yahudawan sahyoniya a barikin Shumira.
A cikin wannan sanarwa an bayyana cewa, wadannan makamai masu linzami sun kai hari kan abin da aka nufa da su.
A cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullah ta fitar ta sanar da cewa, a yau Laraba da karfe 7:20 na safiya Hizbullah ta harba makamai masu linzami 2 na Barkan kan gungun dakarun yahudawan sahyoniyawan a yankin Shtula na yahudawan sahyoniya domin ci gaba da gudanar da ayyukansu na goyon bayan al'ummar zirin Gaza da gwagwarmayar Palastinawa.
A cikin wannan yanayi da misalin karfe 7:15 na safe ne suma dakarun muslunci na kasar Labanon suka kai hari kan wani babban gungun sojojin sahayoniya a garin "Moskfaam" da makamai masu linzami da rokoki.
Har ila yau, wasu majiyoyin yahudawan sahyuniya sun bayyana cewa an ritsa dakarun gwamnatin sahyoniyar a wani harin kwantan bauna a kudancin kasar Lebanon.
Wadannan majiyoyin sun kara da cewa an jikkata wasu adadi mai yawa na yahudawan sahyoniya a arewacin yankunan Falasdinawa da aka mamaye kuma dakarun ceto na jigilar su da jirage masu saukar ungulu akalla 4.
Wasu majiyoyin kuma sun ce wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojojin yahudawan sahyoniya ya sauka a asibitin "Rambam" da ke birnin Haifa.
A halin da ake ciki kuma da misalin karfe 6:00 na safiyar yau ne jiragen yakin gwamnatin yahudawan sahyoniya suka yi ruwan bama-bamai a yankunan Al-Khayam, Kafarkala da Sahl Marjayoun na kasar Lebanon.
Tun safiyar litinin satin daya gabata ne sojojin yahudawan sahyuniya suka fara kai munanan hare hare a yankuna daban daban na kudancin kasar Lebanon, wanda har yanzu ake ci gaba da kai hare hare har zuwa yanzu.
A cewar rahoton ma'aikatar lafiya ta kasar Labanon, hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar daruruwan tare da jikkata wasu dubbai.
Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ba ta yi shiru ba dangane da yadda ake kai wa fararen hula hari a wannan kasa. Ta sanya ajandar yaki da matsugunan yahudawan sahyoniya na mamaya a arewacin Palastinu da aka mamaye, kuma a cikin kwanaki da sa'o'i da suka gabata, ta hanyar harba daruruwan rokoki, sun yi ruwan rokoki kan wuraren gwamnatin sahyoniyawa.