Bayan kammala yakin Uhudu da
komawar kafirai da mushrikai Makkah, sai Imam Ali, tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, wanda shi kadai ne wanda ya tabbatu wajen kare Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama har zuwa lokacin karshe ya zo wajen Manzon Rahama
(SAW) a cikin bacin rai da damuwa. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallama
ya ce: Ali! meyasa kake bakin ciki Ali (a.s) ya ce: “Yaya ba zan yi bakin ciki
ba, alhali Hamza da sauran sojoji sun samu babbar falala ta shahada, ni kuma
wannan nasarar ban sameta ba.
▪️ Imam Ali As, ba wai kawai ba
ya tsoron mutuwa, a’a ba ya ma daukar ta a matsayin abin gudu da rashin kyan
gani, sai dai yana maraba da ita, kuma yana kukan cewa bai samu shahada ba.
Madogara: Muntahal-Amal, juzu'i
na 1, shafi na 427.