1 Agusta 2024 - 12:21
Bayanin Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta Duniya bayan shahadar Dr. Ismail Haniyyah

"Al'umma gwagwarmaya da juyin juya halin Musulunci, suna fatan daukar fansa na Ubangiji da karin samun dacewa da nasara don cimma burin samun cikakkiyar nasara da 'yantar da kasa mai tsarki ta Palastinu daga teku zuwa kogin da kuma kafa kasar Falasdinu tare da zamowar babban birnin Kudus madaukakiya kuma alkibla ta farko ta musulmai a matsayin cibiyarta”.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku cewa: Majalisar Ahlul-baiti (AS) ta fitar da wata sanarwa biyo bayan laifin ta’addanci da gwamnatin sahyoniyawa kan shahadantar da Mujahid mai girma Dr. Ismail Haniyyah.

Bayanin yazo ne kamar haka:

بسم الله القاصم الجبارین

وَ لا تَحسَبَنَّ الَّذینَ قُتِلوا فی سَبیلِ اللَّهِ امواتا بل احیاء عند ربّهم یرزقون

Da sunan Allah Mai Karya Azzalumai

Kuma kada ku dauki waɗanda aka kashe a kan tafarkin Allah a matsayin matattu, bah aka abun yake bas u rayayyu ne a wajen suna masu azurtuwa”.

Majalisar Ahlul-baiti ta duniya ta yi alhinin shahadar fitaccen jagoran gwagwarmaya, dan uwa Abul Abd Ismail Abdus Salam Haniyyah, wanda ya yi shahada a wani kisan gilla na matsorata a safiyar yau da mugayen makiya yahudawan sahyoniya suka aiwatar. Shahid Isma'il Haniyyah ya sadu da shahidan Badar, Hunain, Ahzab da dimbin shahidan yunkurin Husaini wajen fuskantar zalunci da kuma hanyar kawo gyara ga al'ummar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da ma dukkanin shahidan tarihin yunkurin gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, wadanda suka hada da shahid Sheikh Ahmed Yasin, Al-Rentisi, Al-Aroori da... da kuma shahidan bangaren gwagwarmaya irin su shahid Fathi Al-Shaqaki, Shahid Imad Mughniyeh, Abu Mahdi Al-Muhandis da dukkan shahidan gwagwarmayar Musulunci a Palastinu, Labanon, Iraki, Yemen, Siriya, da Afganistan.

 

A matsayinmu na mambobi da masu wa’azin Tabligi kuma masu danfaruwa Majalisar Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) a dukkanin masallatai da makarantu da kungiyoyi da cibiyoyin duniya, muna mika sakon jajantawarmu na wannan babban bala’i da farko ga iyalan wannan shahidin kwamandan wanda suka zamo iyali na jihadi a tafarkin Allah, mai tsayin daka da sadaukarwa ga gwagwarmayar Musulunci a kasar Falasdinu, sannan kuma ga yunkurin gwagwarmayar Hamas mai nasara, daga karshe kuma ga al'ummar Palastinu masu daukaka, musamman al'ummar Gaza, wadanda suke cikin daukaka da jajircewa da tsayin daka suka karya bayan 'yan mamaya, da kuma ga kungiyoyin gwagwarmaya, da al'ummar musulmi da kuma ga jagora Imam Khamene'i mai hikima Muna mika ta'aziyyarmu ga dukkanin masu fafutukar 'yanci da kare adalci da hakki a duniya.

Muna kuma rokon Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wa wannan shahidin kwamanda, da Shahidai sittin daga iyalan Haniyyah da dubun-dubatar shahidan Gaza ya yafe masu ya kuma gafarta musu. Allah ya tashe su a Aljanna mafi daukaka kusa da annabawa da waliyyai na Ubangiji da shahidai da salihai, ya kuma baiwa iyalai da abokan arziki, musamman yunkurin Hamas da Jihadin Musulunci madaukaka a tafarkin jihadi da gwagwarmaya,hakuri mai girma da lada mai yawa

Wannan ba shi ne laifi na farko ba, kuma ba zai zama na karshe ba, kuma ana ci gaba da gwabzawa, in Allah ya yarda, kuma al'umma da gwagwarmaya da juyin juya halin Musulunci, suna fatan daukar fansa na Ubangiji da karin samun dacewa da nasara, don cimma burin samun cikakkiyar nasara wato 'yantar da kasa mai tsarki ta Falasdinu daga teku zuwa kogin da kuma kafa kasar Falasdinu mai hedkwatar Quds Sharif alqiblar musulmi ta farko. Kuma muna rokon Allah da da falalarsa da rahamarsa ya kawo mana Gwamnatin da za ta share fagen kawo karshen mulkin mallaka na yahudawan sahyoniya da Amurka, da na mamaya da sulhuntawa, tare da dawo da martaba da daukakar al'umma da tabbatar da wayewar Musulunci da gwamnatin Mahdi mai daraja ta Musulunci wanda zata girmama musulunci da aahalinsa ta kuma share kafirci da mutanensa da munafunci da mutanensa.

غُلِبَتِ الرُّومُ. فِی اَدْنَی الْاَرْضِ وَهُمْ مِنْ بَعْدِ غَلَبِهِمْ سَیَغْلِبُونَ.فِی بِضْعِ سِنِینَ لِلَّهِ الْاَمْرُ مِنْ قَبْلُ وَمِنْ بَعْدُ وَیَوْمَئِذٍ یَفْرَحُ الْمُؤْمِنُونَ. بِنَصْرِ اللَّهِ یَنْصُرُ مَنْ یَشَاءُ وَهُوَ الْعَزِیزُ الرَّحِیمُ. وَعْدَ اللَّهِ لَا یُخْلِفُ اللَّهُ وَعْدَهُ وَلَکِنَّ اَکْثَرَ النَّاسِ لَا یَعْلَمُونَ  

A karshen bayanin ubangida kuma shugaban shahidai da ‘yantattu jikan manzon Allah Husaini tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi muna muna sake maimaita cewa: “Ya Ubangiji mun yi hakuri da hukuncinka, domin babu abin bautawa da gaskiya sai kai Bamu da wani abin bauta sai kai kuma zamu yi hakuri da hukuncinka. Kai ne mai risker masu kukan ba da wanda zasu kokawa, Ya Kai madawwami na har abada.

انا لله و انا الیه راجعون

Majalisar Ahlul-Baiti (Amincin Allah ya tabbata a gare su).

25 Muharram 1446