A cikin wannan takardar jagoran
juyin juya halin Musulunci ya sake nuna matukar jimamin rashin Hujjul Islam
Al-Hashim tare da yaba halayensa da hidimarsa.
Nassin takardar Jagoran juyin juya halin Musulunci shi ne kamar haka;
Da Sunan Allah, Mai Rahama Mai Jinkai
Mai girma Hujjaul-Islam, Aghaye Haj Sheikh Ahmad Mutahhari, Asal Allah ya dawwamar da hidimarsa
Tare da nuna matukar damuwa da rashin babban limamin Juma'a na Tabriz, marigayi shahidin hidima Hujjatul Islam Al-Hashim, Allah ya jikansa da rahama, wanda babu shakka rashi ne ga al'ummar kasar Azarbaijan, tare da yabawar jama'a ga salon hidimar marigayin; mai girma, wanda ka kasance daya daga cikin mataimakansa da abokan aikinsa, kuma alhamdulillahi, an san ka da kyakkyawan tunani da ayyukanka, na nada ka a matsayina wakilin wannan lardin kuma limamin Juma'a na Tabriz.
Ina fatan matsayin Limamin Juma'a ga al’umma Mumina kuma Jajirtacciya kuma mai Juyin Juya Hali taTabriz zai kasance ka dace da sifofin da suke da su ta hanyar da ta dace, ta fuskar ilimi, ikhlasi, tausayawa da bayyanawa zai zama abin da ka mayar da hankali wajen mu'amala da ma'abota ilimi da kishin kasa na al’ummah mumina musamman ma matasa, da samun huldar alaka ta gaskiya da ta kamata a ko da yaushe ka yi la'akari da manyan malaman da malaman jami’a, malamai da kungiyoyin juyin juya hali da tausayawa masu sadaukarwa ga raunanan al'umma. Ina rokon Allah ya ba ku nasara.
Sayyid Ali Khamenei