Yayin da harkar Musulunci ta ke ta bunkasa a Najeriya, saboda
tasirin da sahyoniyanci da wahabiyanci ke da shi a kasar 'yan Shi'a a Najeriya
sun fuskanci takura da tsangama da dankwafewa da karfin yan sanda ko soja. A
shekarar 2014 (1395) hukuma ta kai wani hari kan mutanen da suke muzaharar
Kudus ina ya yi sanadin shahadar mutane da dama, ciki har da ‘ya’yan Shaikh
Zakzaky uku.
Bayan shekara guda (2015) da faruwar hakan kuma bayan dawowar Shaikh Zakzaky daga tafiyarsa zuwa Iran, hukumar najeriya ta hannun sojojinta sun aukar da kisa inda suka zubar da jinin ‘yan shi’a a Husainiyyah Baqiyatullah Zaria, inda suka tarwatsa taron da ake fara gudanarwa na dora tutar mauludin manzon Allah (sawa) a Husainiyyar. A wanna harin baya ga kashe wasu adadi na 'yan Shi'a, sun kashe ‘ya’yan Shaikh Zakzaky guda uku wanda suma sukai shahada a wannan hari wanda yaran shekh din an kashe su ne a gidansa bayan da sojojin sun kai harin har gidan nasa da ke unguwar Gyallesu Zariya inda suka kama Shaikh Zakzaky da matarsa da sauran 'yan Shi'a da dama suka daure su.
Duk da cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky ya jima gidan yari har zuwa shekarar 2022, sai dai harkar Musulunci a Najeriya ta samu kafuwa da ci gaba da rayuwa da yaduwa daram a Najeriya. A karshe dai babbar kotun kasar ta wanke Shekh Zakzaky daga dukkan laifukan da ake tuhumarsa da shi, inda a yanzu aka san shi a matsayin alama abun koyi ta jihadi da gwagwarmaya.
Babban shugaban Harkar Musulunci a Najeriya a wata hira ta musamman da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (a.s) – Abna- na kasa da kasa baya ga takaitaccen tarihin rayuwarsa, ya yi tsokaci kan darussa na jihadi da gwagwarmaya wanda ya koye su daga Mazhabar Ahlul Baiti (a.s.) kuma ta mahangar musamman da soyayya ta musamman ga Imam Khumaini (RA) wanda shi ne abin koyi kuma malaminsa a wannan tafarki.
Ga Yadda Ganawar Da Tattaunawar Ta Kasance:
Abna: Da Farko Muna So Ku Yi Mana Bayani Game Da Rayuwarku:
Shekh Zakzaky: An haife ni a gidan addini ma’abocin riko da bin shari’a Mahaifina da kakana malaman Alqur'ani ne. Tun farko na koyi darussan addini da harshen larabci a wajen mahaifina da kakata, da kuma sauran malamai. Ina da shekara 15 na tafi makarantar horas da malamai na kananan makarantu sannan bayan na yi karatu na tsawon shekaru biyu a wannan makarantar na yi wata makaranta a Kano na yi karatu a can na yi shekara biyar na zama malamin firamare. Ban da karatu a makarantar zamani, na koyi koyarwar addini a wurin shehunan malamai kuma ina da shekara 24 na je jami’a na karanta tattalin arziki na kuma kammala.
Abna: Ta Yaya Kuka San Mazhabar Ahlul Baiti Da Juyin Juya Halin Musulunci?
Baya ga karatun jami'a, ban yi sakaci da karatun addini ba, na ci gaba da karatu fannin ilimin addinin Musulunci a wajen wasu malamai. A cikin saba'inoni, lokacin da nake jami'a, kuma a daidai lokacin da Imam Khumaini (RA) yake a birnin Paris, na sami labarin yunkurin juyin juya halin Musulunci na Iran, kuma na bibiyi abubuwan da suke faruwa ga wannan juyin.
Na zo Iran a karon farko a ranar taron farko na zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci, kuma na kasance mai aikin isar da Addinin Musulunci tun daga lokacin zuwa yanzu. Ina bibiyar jawaban Imam Khumaini (RA) a harsunan Larabci da Ingilishi tun yana birnin Paris. Kafin nasarar juyin juya halin Musulunci na kasance ina aiki a cikin kungiyar dalibai musulmi kuma na kasance babban sakataren wannan kungiya. Lokacin da muka san Imam Khumaini (RA) sai muka gane cewa Imam Rahal ya tabbatar da dukkan abunda mu ke da buri...
AKwai Ci Gaba