24 Mayu 2024 - 19:27
Hamas Ta Sanar Da Kame Wani Babban Jami'i Na Sojojin Mamaya A Ranar 7 Ga Watan Oktoba

A ranar 2 ga Disamba, 2023, sojojin mamaya suka tabbatar da mutuwar Hamami, kuma ta hanyar buga hakan a dandalin "X" cewa Kanar Assaf Hamami (mai shekaru 41), kwamandan Kudancin Brigade na Gaza, daga Kiryat Ono (tsakiya), an kashe shi a ranar 7 ga Oktoba. Kuma An ajiye gawarsa a zirin Gaza.” Sanarwar ta yi nuni da cewa jami'an sojojin mamaya sun sanar da iyalan jami'in mutuwarsa.

Cikin jumlar da ke cewa:, "Jagorancin da ya bar kwamandojin sojojinsa a wajen garkuwa" Al-Qassam ta ɗorawa Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, Ministan Tsaro Yoav Gallant, memba na Majalisar Yakin Benny Gantz, da Babban Hafsan Sojoji Herzi Halevy alhakin barin Hamami a cikin garkuwa da shi tare da rashin damu da makomarsa.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Rundunar Qassam reshen soja na kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas ta sanar da cewa, kwamandan runduna ta kudu a yankin Gaza na sojojin mamayar Isra'ila, Assaf Hamami, an kama shi ne a ranar bakwai ga watan Oktoban bara.

Hakan ya zo ne ta wani sabon faifan bidiyo da Al-Qassam ta watsa - Alhamis - tana bayyana cewa an ji masa rauni yayin da aka kama shi, wanda ta haifar da rashin tabbas game da makomarsa a yanzu.

Cikin jumlar da ke cewa:, "Jagorancin da ya bar kwamandojin sojojinsa a wajen garkuwa" Al-Qassam ta ɗorawa Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, Ministan Tsaro Yoav Gallant, memba na Majalisar Yakin Benny Gantz, da Babban Hafsan Sojoji Herzi Halevy alhakin barin Hamami a cikin garkuwa da shi tare da rashin damu da makomarsa.

Ta kammala faifan bidiyon da maudu’in cewa “Lokaci yana kurewa” wanda ta rika sakawa akai-akai, dangane da kara raguwar lokacin da ake da shi na kulla yarjejeniyar musaya da karuwar fursunonin Isra’ila da ake kashewa a Gaza sakamakon mummunan harin bama bamai da sojojin mamaye suke jefawa.

A ranar 2 ga Disamba, 2023, sojojin mamaya suka tabbatar da mutuwar Hamami, kuma ta hanyar buga hakan a dandalin "X" cewa Kanar Assaf Hamami (mai shekaru 41), kwamandan Kudancin Brigade na Gaza, daga Kiryat Ono (tsakiya) , an kashe shi a ranar 7 ga Oktoba. Kuma An ajiye gawarsa a zirin Gaza.”

Sanarwar ta yi nuni da cewa jami'an sojojin mamaya sun sanar da iyalan jami'in mutuwarsa.