Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku tsakure kuma takaitaccen bayanai na Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon wanda yayi a yau juma'a:
A cikin siyayar kasashen waje, a cikin shekaru 3 da suka gabata, mun sami ci gaba sosai
Sayyid Raisi Ako da yaushe yana kara jaddada cewa ya kamata a bai wa kasashe makwabta, kasashen Larabawa, makwabta daban-daban fifiko, kusanci da Rasha da Sin ba tare da ja da baya ba tare da yanke hulda da kasashen yamma. Babban abin da aka ba da fifiko shi ne kulla alaka da kasashen yankin da na makwabta da na gabashi tare da tabbatar da 'yancin kai da ikon kasar Iran.
A dangane da batun Palastinu, kuwa Shahid Raisi, baya ga riko da akidu da matsayi na Jamhuriyar Musulunci, to amma a mahangar kashin kansa yana da mahanga ta musamman ga Palastinu na da kuma kiyayya mai girma ga gwamnatin sahyoniya.
Ya kasance yana da cikakken imani da gwagwarmaya da yunkurorin gwagwarmaya, ya yi imani cewa gwagwarmaya ita ce kadai hanyar kawar da wannan zalunci mai girma. Wannan wani bangare ne na addini da imanin Ayatullah Raisi, shi ya sa muke ganin wannan akida a wurinsa tun daga farko. A lokacin da ya zama shugaban kasa, ya yi aiki tare da ba da hadin kai da taimako iri-iri ga gwagwarmaya.
Mafi muhimmanci siffofin da wadannan mutane guda biyu suke da ita, ita ce tawali'u, son talaka, mabukata, da wanda ake zalunta, da 'yan gwagwarmaya da mujahidai.
Sayyid Hasan Nasr'Allah
Shahadar shugaban Iran da sahabbansa lamari ne mai radaɗi.
Mun dauki aniyar kin gudanar da bukukuwan da suke da alaka da nasarar gwagwarmaya.
A bangare ln alakoki na siyasa abu ne mai wahala ace ministan harkokin wajen kasar ya iya zuwa ya tattauna da shugabanni da sarakuna a lokaci guda kuma ya yi magana da dakarun jama'a da masu gwagwarmaya, abu ne da ke bukatar kokari sosai.
Wasu mutane suna ƙin talakawa suna guduwa zuwa fadojinsu, amma waɗannan ƙaunatattun mutanen biyu ba haka suke ba, soyayyarsu, ransu yana tare da talakawa da waɗanda ake zalunta.
Wannan ita ce mazhabar Musulunci, wannan ita ce mazhabar Annabi da Ahlul-baiti, wannan ita ce mazhabar Imam Khumaini, wadanda a kullum suke magana a kan talakawa da mazauna bukkoki.
Muna bukatar ababen koyi irin wadannan, wajen kokarin jajircewa, wajen rashin gajiyawa, cikin tawali'u da soyayya.
Jana'izar Rakiyar Gawar Shahidi Raisi Ita Ce Rakiyar Gawa Mafi Yawa Ta Uku A Tarihin Duniya
Babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon a wajen taron tunawa da shahid shugaban kasar Iran da sahabbansa:
Wasu kafafen yada labarai na yammacin duniya da na larabawa sun yi ta tallata cewa al'ummar Iran ba za su halarci taron jana'izar shugaban kasar ba kuma za su juya baya.
Hotunan jana'izar sun fito fili kuma kowa a fadin duniya ya shaida hakan.
Ta fuskar inganci da yawa, an yi jana'izar shahidi Raisi bayan jana'izar Imam Khumaini da Haj Qasim kuma ba a taba yin irinta ba.
A tarihin bil'adama da duniya ba a taba ganin irin wannan jana'izar da shelanta riko da tsari da shugabanci ba, wannan sako ne mai karfi ga abokai da makiya.