24 Mayu 2024 - 15:31
Sakon Ta'aziyyar Miliyoyin Al'ummar Kasar Yemen Ga Iran A Cikin Gangamin Da Suka Yi Na Nuna Goyon Bayan Ga Zirin Gaza

Al'ummar kasar Yemen wadanda a yau (Juma'a) a mako na talatin da biyu a jere a larduna daban-daban na kasar sun halarci zanga-zangar nuna goyon baya da taimakawa ga al'ummar Gaza kuma sun gabatar da sakamakon da ta'aziyyarsu ga jagora da gwamnati da al'ummar kasar Iran, saboda shahadar shugabanta da sahabbansa a hatsarin jirgin sama daya faru.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: bisa nakaltowa daga kamfanin Dillancin na -IRNA- shima bisa nakaltowa daga kafofin yada labarai na Yamen cewa: bayanin wannan muzaharar yana dauke da cewa: Muna mika ta'aziyyarmu ga shugabanni da gwamnati da al'ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da shahadar Ayatullah Sayyid Ibrahim Raisi, shugaban kasar da sahabbansa cikin mummunan hatsarin abin ya faru, kuma mun yi tarayya da su a cikin wannan bakin ciki.

Al'ummar wannan kasa a yau Juma'a sun gudanar da zanga-zanga a larduna daban-daban na Saada, Marib da Rima tare da taken "Mun tsaya kyam ga Gaza, ana ci gaba da yin jihadi".

An gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al'ummar Gaza cikin mutane miliyan guda a Saada, kuma a karshen wannan tattakin an fitar da wata sanarwa da ke jaddada ci gaba da goyon bayan al'ummar zirin Gaza.

A cikin bayanin da aka bayar, an yaba da ayyukan da sojojin Yaman suke yi kan gwamnatin sahyoniyawan, da kuma irin jaruntakar ayyukan gwagwarmayar Musulunci a Palastinu, Labanon da Iraki.

A cikin wannan bayanin, an bukaci jama'a da halartar sansanonin horarwa don samun kwarewar yaki da kuma ba da izinin yin yaki kai tsaye tare da mayakan Falasdinawa masu yakar gwamnatin sahyoniyawan.

Masu zanga-zangar na Yemen sun kuma yi kira ga al'ummar duniya masu 'yanci da su yi amfani da makamin takunkumin karya tattalin arziki kan kayayyakin Amurka da Isra'ila da kamfanonin da ke tallafa musu.

Dangane da haka ne kakakin rundunar sojojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya bayyana a cikin jawabinsa a wajen wannan taro na miliyoyin jama'a cewa an kai hare-hare 3 kan wasu jiragen ruwa 3 masu alaka da gwamnatin sahyoniyawan.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, a cikin watannin da suka gabata, domin nuna goyon baya ga gwagwarmaya da al'ummar Palastinu suke yi a zirin Gaza, sojojin kasar Yemen sun kai hari kan wasu jiragen ruwa na Amurka, Birtaniya da yahudawan sahyoniya ko kuma wasu jiragen ruwa da suka nufi yankunan da aka mamaye a cikin tekun Bahar Maliya da Mashigar Bab Al Mandeb. Dakarun sojojin Yaman sun yi alkawarin kai farmaki kan jiragen ruwan wannan gwamnati ko kuma na jiragen da ke zuwa yankunan da ake mamaya a cikin tekun bahar maliya har sai lokacin da gwamnatin sahyoniyawan ta daina kai hare-hare a zirin Gaza ba.