Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: An fara taro karo na 19 na shugabannin tsarin shari'a na kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a birnin Tashkent na kasar Uzbekistan.
A farkon wannan taro, manyan mahukuntan shari'a na kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai sun yi shiru na minti daya don girmama shahadar Ayatullah Raisi, shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Amir Abdullahian, ministan harkokin wajen kasar Iran, da sauran shahidai.