Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Jiya da yamma ne sojojin Yaman suka harbo wani jirgin yakin Amurka maras matuki kirar MQ9 a lokacin da yake gudanar da wani mummunan hari a sararin samaniyar lardin Marib.
Wannan jirgi maras matuki na dala miliyan 32, shi ne jirgi mara matuki na hudu da aka harbo a lokacin yakin "Nasarar Alkawari" da "Jihadi Mai Tsarki don Tallafawa Gaza".
Wannan jirgi mara matuki dai an harbo shi ne da makami mai linzami wanda ake harbawa daga kasa zuwa sama da kasar Yemen ta kera, kuma za a buga hotunansa nan ba da jimawa ba.


