20 Yuli 2023 - 06:47
Syria: An Kakkabo Jirage Marasa Matuka Na 'Yan Ta'adda Guda Uku

Syria ta sanar da kakkabo jirage marasa matuka na 'yan ta'adda guda uku a cibiyar kasar

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Ma'aikatar tsaron kasar Siriya ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuka guda uku mallakar 'yan ta'adda a tsakiyar kasar.

Ma'aikatar ta sanar da cewa, rundunonin sojin kasar sun lalata jiragen yaki marasa matuka guda uku da ke dauke da ababen fashewa a yammacin birnin Aleppo.

Har ila yau, sojojin na Syria sun lalata wani makami mai linzami na kungiyoyin 'yan ta'adda, wadanda aka yi amfani da su wajen kai farmaki kan kauyuka da ke kusa da Idlib.

Wannan harin dai ya faru ne bayan rikici tsakanin sojojin Siriya da 'yan ta'addar 'yan adawa bayan zaman lafiya na kwanaki biyu a arewa maso yammacin Siriya.