Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Majalisar tana bada wannan rahoton ta hukumar OCHA wanda kuma yayi dai dai da rahoton da gwamnatin Falasdinawa a Ramalla ta bayar a jiya Asabar.
Rahoton ya kara da cewa daga lokacin zuwa yanzu gwamnatin yahudawan ta rusa gine-ginen Falasdinawa har 8,746 daga lokacin, sannan gwamnatin Yahudawan ne suka rusa gine-ginen da kansu ko kuma sun tilastawa masu gine0ginen su rasasu da kansu don kada ta dora masu biyan kudade masu yawa idan ta rusa gidajen da kanta.
Rahoton ya kara da cewa wannan dai ya tilastawa Falasdinawa 13,000 zama yan gudun hijira, sannan wasu 152,000 suka yi asarar dukiyoyinsu. Gwamnatin yahudawan sukan rusa gidajen ne da sunan an gina sub a bisa ka’isa ba, kuma mustahili ne gwamnatin yahudawan ta bawa wani bafalasdinu izinin gina daga a yankunan Falasdinawa da ta mamaye
342/