Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (AS) - ABNA - ya habarta cewa, Ayatullah Sheikh Mohammad Naseri daya daga cikin fitattun malaman da ke koyar da darasin AKhlak kuma malamin makarantar Isfahan, ya yi bankwana da da gidan duniya a jiya Jumaa.
Bayanin da aka fitar daga ofishin Ayatullah Naseri daya daga cikin fitattun malaman Akhlak kuma malami a makarantar Isfahan, ya zo kamar haka;
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
انا لله و انا الیه راجعون
A wannan loakci muke sanar da al'ummar muminai da masu kaunarmu wafatin Ayatullahi Nasiri (Allah Ya Haskaka makoncinsa) muna masu rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya jikansa da rahama.
Nan gaba za a bayyana jadawalin lokutan da gabatar da jana'izar marigayin.