26 Mayu 2022 - 19:56
​The New York Times: Isra'ila Ta Sanar Da Amurka Cewa Ita Ce Ta Kashe Sayyad Khodaei

Majiyoyin leken asirin Amurka sun bayyana cewa Isra'ila ta sanar da Washington cewa ita ce ta kashe daya daga cikin jami’an IRGC na Iran Kanar Hassan Sayyad Khodaei, kamar yadda jaridar New York Times ta ruwaito a ranar jiya Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cewar jaridar, kisan Khodaei na da nufin zama "gargadi ga Iran" don dakile "kashe wakilan hukumomin Isra'ila."

Majiyar jaridar ta bayyana cewa, Khodaei yana cikin jagorancin sashin sirri na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da Isra’ila ke zargi da aikata wannan aiki.

Tun da farko dai an bayyana cewa, a ranar 22 ga watan Mayu wasu da ba a san ko su wanene ba suka harbi motar Khadaei da bindiga a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa gidansa a wani layin da ke gabashin birnin Tehran. Mutane biyu akan babur ne suka kai harin, inda suka harbe jami’in na IRGC har sau biyar.

Ofishin yada labarai na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana lamarin a matsayin aikin ta'addanci. Shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi ya fada a ranar Litinin cewa hukumomin kasar za su dauki fansa kan kisan da aka yi wa kanar din ta hanyoyin da suka dace.

342/