1 Mayu 2022 - 19:21
Najeriya: Lawal Ya Bukaci A Sasanta Da ASSU A Ranar Ma’aikata

Shugaban majalisar dattawan tarayyar Najeriya Ahmed Lawal ya godewa ma’aikata a Najriya dangane da gudumawar da suke bayarwa don ci gaban kasar, a dai dai lokacinda ake bukukuwan ranar ma’aikata a yau Lahadi 1 ga watan Mayu na wannan shekara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar leadership ta Najeriya ta nakalto mai bawa shugaban majalisar shawara kan al-amuran watsa labarai Ola Awoniya yana fadar haka a jiya Asabar a wata sanarwa da ya fitar.

Labarin ya kara da cewa shugaban majalisar dattawan ya bukaci a warware matsalar da ke faruwa tsakanin kungiyar ASSU ta malaman makaranta da kuma gwamnatin tarayyar don a samu a sake bude jami’o’in kasar da gaggawa.

Kungiyar ASSU ta malaman jami’o’I a Najeriya suna yajin aikin kimani watanni biyu kenan, saboda rashin cika alkawarin da gwamnatin tarayya kasar ta yi masu a shekarun da suka gabata, na hakkokinsu da kuma kyautata yanayin karatu a jami’I’o’in kasar.

342/