15 Afirilu 2022 - 13:45
Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Kungiyar "Mahmoud Al-Sarkhi" A Iraki/ An Rufe Ofisoshinta A Larduna Da Dama.

A yammacin ranar Talata ne masu zanga-zangar kasar Iraki suka rufe tare da kona mafi yawan ofisoshi da helkwatar kungiyar a larduna daban-daban na kasar Iraki, inda suka ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa da kungiyar ta "Mahmoud Al-Sarkhi".

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo labarin cewa, a yammacin ranar Talata masu zanga-zangar kasar Irakin sun ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kungiyar "Mahmoud al-Sarkhi" inda suka rufe tare da kona mafi yawan ofisoshi da helkwatarta a larduna daban-daban na kasar Iraki.

A wata hira da jaridar Sumaria, wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, wasu da dama daga cikin mazauna gundumar al-bayy da ke birnin Bagadaza sun rufe ofishin wannan karkatacciya kungiya.

Majiyar ta kara da cewa: Masu zanga-zangar sun kuma kona ofisoshin Al-Sarkhiyah da ke Diwaniyah, Al-Samawah da Babil.

A cewar wata majiyar tsaro, 'yan kasar Irakin da ke zanga-zangar sun kuma kona helkwatar al-Shamiya, Diwaniyah, da wasu sansanonin al-Samawah da Babil.

Baya ga birnin Basra, an kuma gudanar da zanga-zanga a wadannan larduna don nuna adawa da karkatattun akidun wannan yunkuri na karkatacciyar hanya na wannan kungiya

A sa'i daya kuma, shugaban majalisar koli ta shari'a ta kasar Iraki Faeq Zidan, ya bayar da umarnin kame dukkan mabiya tafarkin Mahmoud al-Sarkhi da ke bin wannan karkatacciyar hanya.

Idan dai ba a manta ba, sabuwar takaddamar ta fara ne a lokacin da ‘Ali Musa Aqul Kazem Al-Masoudi’ mai wa’azin masallacin ‘Al-Fatah Al-Mubin’ da ke birnin ‘Al-Hamza Al-Gharbi’ na lardin Babil, wanda mabiyin addinin ne dake bin "Mahmoud Al-Sarkhi",a garin Babil. a ranar Juma'ar da ta gabata a yayin da ake gabatar da hudubobin Juma'a na wannan masallaci, yayi kira da a ruguza dukkan wuraren ibada da kaburburan annabawa, limamai da malaman addini. Wannan Abun dai ya haifar da kakkausar suka da kuma tofin Allah tsine a cikin al'umma da na siyasa a kasar Iraki, sannan baya ga zanga-zangar da tarukan da aka yi a gaban ofisoshin jam'iyyar Jama'atul Sarkhi, zanga-zangar ta barke a shafukan sada zumunta.

Dangane da haka ne kafafen yada labarai na kasar Iraki suka bayar da labarin a ranar Talatan kan zanga-zangar da mazauna yankin Al-Hamza da ke birnin Babil suka yi da kuma rufe dukkan ofisoshin jama'atul-Sarkhi bisa umarnin 'yan sandan lardin. Bayan zanga-zangar da mazauna Al-Hamza suka yi a gaban ofishin Jamaat Al-Sarkhi, rundunar 'yan sandan Babila ta kai ga masu zanga-zangar tare da amsa bukatunsu.

Haka kuma wasu da dama daga cikin mazauna birnin Qasim da ke lardin Babil sun kai hari a hedikwatar Jama'atu Sarkhi da ke birnin, inda suka cinna mata wuta, kuma da haka suka mayar da martani ga kalaman Khatibi na yin kira da a ruguza kaburburan Imamai da wuraren ibada na birnin.

A daren jiya ne wasu da dama daga cikin mazauna lardin Dhi Qar da ke tsakiyar lardin wato birnin Al-Nasiriyah suka kai farmaki kan ofishin Al-Sarkhi da ke wannan birnin tare da nuna adawa da shi.

Sai dai watakila za a iya cewa mayar da martani mafi karfi yazo ne daga gargadin da Muqtada al-Sadr, jagoran kungiyar Sadr, a jiya in da gargadi Mahmoud al-Sarkhi da ya sake sakin Kalaman barranta daga abubuwan daya fada ta hanyar Ali Musa Agul na tsawon kwanaki uku, idan ba haka ba zai kasance da kanshi bisa tsarin addini, lamirnsa da kuma doka bisa al'adar da ta dace ta al'umma zai shiga wannan zanga-zangar adama da shi. Ya jaddada cewa bai kamata a yi watsi da yadda ake yada gurbatattun tunani a cikin al'ummar Iraki ba.

Ba zato ba tsammani "Mahmoud al-Sarkhi" ya bayyana a shekara ta 2003 kafin kifar da gwamnatin Saddam, hambararren shugaban kasar Iraki, kuma ya gabatar da kansa a matsayin daya daga cikin Marajio'in addini na Iraki a matakin Ayatollah. Duk da cewa ba shi da wani matsayi mai girma na ilimi, Al-Sarkhi ya gabatar da kansa a matsayin dalibin Ayatollah Shahid Mohammad Baqir Sadr da Ayatullah Sistani, kuma ya fara ayyukansa a shekara ta 2003 (yana dan shekara 40) da da'awar cewa shi "Maraji'i" ne a Iraki. Yana da’awar cewa shi Ayatullahi ne kuma Ayatullah a cikin fikihun ‘yan Shi’a wanda ya kai matakin ijtihadi, amma babu wani Maraji'i ko Ayatollah da ya shaida cewa ya kai wannan matakin.

Yana da kyau a san cewa magoya bayan "Mahmoud Al-Sarkhi" na daga cikin wadanda suka kai harin kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Karbala a watan Nuwamban shekara ta 2019.

342/