18 Maris 2022 - 19:02
Ana Bukatar Dala Biliyan 350 Don Bunkasa Samar Da Wutar Lantarki Da Rarrabata A Nahiyar Afrika

Rahoton da cibiyar samar da makamashi ta kasar birtaniya ta fitar ya nuna cewa kasashen Afrika na kudu da Hamadar sahara za su bukaci zuba hannun jari har dala biliyan 350 daga yanzu zuwa shekara ta 2030 kafin su iya inganta samar da wutar lantarki da rarrabawa da kuma shawo kan matsalar wutar lantaki da yankin ke fama da shi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Har Ila yau ya zo a cikin rahoton cewa wannan damar ta sanya hannun jari tana aiki ne tare da cibiyoyin kudi wanda wasu kamfanoni na gwamnatin a kasashen Afrika na kudu da hamadar sahara suka samar, domin karfafa wata ma’ajiya ta samar da wutar lantarki ga gidaje da kasuwan da masana’antu da ake samar da su ta hanyar rarrabasu.

Bukatar wutar lantarki a yankin Afrika na kudu da sahara ya kara rubanyawa a cikin shekary 15 d , kuma ana tsammanin zai karu sosai har sau 8 nan da shekara ta 2050, yace wannan tsananin bukatar ta samu asali ne sakamakon ginshikan abubuwa guda 3 karuwar yawan jama’a da kuma yadda mazauna ke yin hijira zuwa birane da kuma canje-canjen da ake samu a bangaren tattalin arziki.

342/