30 Janairu 2022 - 17:11
​Iran: Ra'isi Da Macron Sun Tattauna Ta Wayar Tarho Kan batutuwa Da Suka Shafi Tattaunawar Vienna

Shugaba Ebrahim Raeisi na Iran ya bayyana ginshiƙai uku na yuwuwar cimma yarjejeniya tsakanin Iran da bangaren da ke halartar tattaunawar Vienna kan shirin Iran na nukiliya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da yake magana ta wayar tarho tare da takwaransa na Faransa Emanuel Macron a ranar jiya Asabar, Raeisi ya bayyana matsayin Iran kan batun cire mata takunkumi a matsayin gishikin samun duk wata nasara a wannan tattaunawa.

Shugaban na Iran ya ce: "Duk wani kokari daga daya bangaren da ya kamata ya ginu ne a kan wannan mahanga. Shugaban na Iran ya ce "Jamhuriyar Musulunci ta riga ta tabbatar da kudurinta da kuma muhimmancinsa wajen ganin an cimma wannan yarjejeniya."

Bangarorin da ke halartar tattaunawar dai sun hada da Birtaniya, Faransa, Rasha da Jamus, da sauran bangarorin dasuka rattaba hannu kan yarjejeniyar 2015 da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Amurka ta yi watsi da yarjejeniyar a cikin 2018 kuma ta mayar wa Iran da takunkumin da yarjejeniyar ta janye mata.

Tun a karshen shekarar da ta gabata ne dai Iran da sauran bangarorin suka koma kan teburin tataunawa zagaye takwas a birnin Vienna na kasar Austria, domin yin nazarin yuwuwar cire mata takunkumin.

342/