Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A ranar Litini, ministan harkokin wajen kasar ta Togo, ya gana da shugaba Ebrahim Ra’isi.
Yayin ganawar shugaba Ra’isi, ya ce Afrika nahiya ce da ta kunshi albarkatu da arziki da daman a al’umma da kuma na karkashin kasa, kuma Iran a shirye ta ke ta karfafa alakarta da Afrika ciki har da kasar ta Togo domin amfanin juna.
Shi kuwa a nasa bangare ministan harkokin wajen kasar ta Togo, Robert Dussey, ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta karfafa alaka da Iran.
Ya kuma ce suna neman hanyoyin zurfafa alaka da Iran a fagage da dama domin cin moriyar juna.
342/