8 Janairu 2022 - 18:16
Ra'isi: Muna Samun Nasara A Matakan Yaki Da Cutar Corona A Iran

Shugaba Ra'isi an Iran ya ce ana samu gagarumar nasara wajen yaki da cutar corona a fadin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wani bayani da ya gabatar a yau a zaman da ya yi da jami'an kiwon lafiya dangane da halin da ake cikia kasar wajen yaki da yaduwar cutar corona, shugaba Ra'isi an Iran ya bayyana cewa, an samu babban ci gaba a wannan fage.<p "="">Ya ce a halin yanzu kusan daukacin mutanen kasars un samu allurar rigafin corona kashi na farko da na biyu, yayin da kuam yanzu ana ci gaba da gudanar da zagaye na uku.<p "="">Dangane da yaduwar cutar ya ce, idan aka kwatanta da lotan baya a halin yanzu za aiya cewa an karya lagonta a cikin kasar, domin kuwa baya daruruwan mutane ne suke mutuwa a kowace rana, dubbai masu yawa kuma suna kamuwa kullum rana, amma a yanzu mutane kasa da talatin suke mutuwa maimakon dari bakawai ko dari takwas, wanda a cewarsa,, shi ma da yardar Allah za a kawo karshenta, ta yadda za a daina samun asasar rayuka.

342/