Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya bayyana haka ne a yau Laraba a lokacinda yake halattan taro na majalisar kare hakkin bil’adama na kasar Iran a ma’aikatar shari’ar kasar a nan birnin Tehran.
Mohseni-Ejeie ya kara da cewa kasar Iran ce zata nunawa duniya menene hakkin bil’adama, ba kasashen yamma wadanda suka shahara a ayyukan cin mutuncin bil’adama ne zasu nuna mana menen hare hakkin bil’adama ba.
Alkalin alkalan ya kammaka da cewa a halin yanzu kasashen yamma sun maida batun kare hakkin bil’adama a matsayin makami na yakar gwamnatin jumhuriyar Musulunci ta Iran a duniya, a dai lokacin babu wata kasa a duniya a yau face tana fuskantar wani nau’I na cin mutuncin bil’adama daga wadannan kasashe.
A yau kasashen yamma su ne a gaba wajen takurawa kasashen duniya da dama, da sunan kare hakkin bi’adama amma sojojin su da makirce-makircensu da danniya da kuma kissan mutanen ba basu san hawa ko sauka ba ya zama al-ada a garesu.
342/