Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- A wata hira da ya yi da tashar Al-Hadath ta Saudiyya, Al-Burhan ya ce, batun hulda da Isra'ila ya zama wajibi domin hakan ya bayar da damar komawar Sudan cikin kasashen duniya," in ji shi.
Al-Burhan ya bayyana karara cewa kasarsa ba ta da makiya, saboda haka wajibi ne Sudan ta tabbatar wa duniya cewa kofarta a bude take ga kowace kasa ta duniya.
Wannan furuci na zuwa ne kasa da wata guda bayan da Al-Burhan ya nada tsohon dan majalisa Abu Al-Qasim Muhammad Bartam a matsayin mamba a sabuwar majalisar mulkin rikon kwarya.
An san Abu al-Qasim Muhammad Bartam a matsayin daya daga cikin fitattun mutanen Sudan da ke goyon bayan kulla hulda da Isra’ila cikin gaggawa.
Kasar Sudan dai na fama da zanga-zanga tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah Al-Burhan a ranar 25 ga watan Oktoba, lokacin da ya rusa dukkanin hukumomin gwamnatin rikon kwarya tare da hambarar da abokan aikinsa na farar hula da yake tare da su, tun daga lokacin da suka cimma wata yarjejeniya a shekarar 2019 bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.
342/