Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ya ce babban masanin ya bada muhimmiyar gudunmawa a shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, wanda duk da barazana da takunkumin da shirin yake fuskanta na tsawon shekaru 20 amma ba’a taba tsayawa da aiki ko da minti daya ba .
Ya ce makiya jamhuriyar musulunci sun dade suna kokari wajen ganin bayan juyin musulunci na Iran na baya bayan nan shi ne kokarin da Amurka tayi ta hanyar Amfani da Takunkumin Tattalin Arziki na ta’addanci.
Daga karshe ya nuna cewa Iran ta bayyana gaskiyarta game da shirinta na nukiliya dake tabbatar da cewa na zaman lafiya ne zalla , ta hanyar tattaunawa da kuma sanya hannu kar yarjejeniyar NPT ta hana yaduwar makan kare dangi.
342/