7 Nuwamba 2021 - 11:47
Yemeni:Sojojin Sun Kwace Iko Da Wani Sansanin Sojojin Saudiya Mai Muhimmanci A Ma’arib

Sojojin kasar Yemen tare da kwamitocin sojojin sa kai masu taimaka masu sun kwace iko da wani sansanin sojojin Saudiya a Ma’arib daga kudancin kasar a jiya Jumma’a.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wata majiyar sojojin na Yemen wacce ba ta son a bayyana sunanta ta na cewa, da farko sun yi luguden wuta da makamai masu linzami da kuma igwa kan sansanin sojojin UmReesh na sojojin Saudiya, sannan suka yi masa kawanya ta ko ina. Daga nan sojojin Saudiya, ba su da zabi in banda janyewa daga wurin.

Labarin ya kara da cewa sansanin Sojojin Saudiyya na UmReesh ya na kusa da wuraren har makamashi a lardin na Ma’arib. Kuma gwamnatin Abdurabbu Mansur Hadi ta na samun arziki mai yawa daga wurin.

342/