6 Nuwamba 2021 - 13:23
​Kamalvandi: Sanadarin Uranium Da Iran Ta Tanada Kashi 60% Ya Kai Kilogiram 25

Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) Behrouz Kamalvandi ya ce adadin Uranium da kasar ta tanada kashi 60%, ya kai kilogiram 25, yana mai cewa Iran ta kuma samar da sinadarin Uranium sama da kilogiram 210 na kashi 20%.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Da yake magana a gefen baje kolin nasarorin da Iran ta cimma a birnin Tehran a jiya Juma'a, Kamalvandi ya ce, shirin dabarun yaki da takunkumi da ke cikin dokar da majalisar dokokin Iran ta zartar a watan Disamban da ya gabata, ta baiwa hukumar makamashin nukiliya ta Iran AEOI damar bunkasa ayyukanta na nukiliya domin ayyukan farar hula.

A ranar 1 ga Disamba, 2020, 'yan majalisar dokokin Iran sun kada kuri'a da gagarumin rinjaye na amincewa da shirin, wanda ya dora wa gwamnatin kasar alhakin dakatar da yin aiki da wasu alkawurra karkashin yarjejeniyar nukiliyar 2015, wadda aka fi sani da Joint Comprehensive Plan of Action (JCPOA).

Tuni dai Washington ta janye daga yarjejeniyar a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasar Donald Trump a ranar 8 ga watan Mayun 2018, kuma kasashen Turai da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sun ki cika alkawurran da suka dauka a karkashin JCPOA, wanda hakan ne yasa Iran ita ta dauki irin wannan matakin domin mayar da martani.

A bisa dokar majalisar, an bukaci AEOI ta samar da akalla kilogiram 120 na sinadarin uranium a duk shekara, yayin da kuma a halin yanzu bukatun kasar take da ya haura na kilogiram 210, in ji Kamalvandi.

342/