30 Oktoba 2021 - 16:49
​Sojojin Isra’ila Sun Jikkata Falasdinawa Masu Zanga-zangar Adawa Da ci Gaba Da Gina Matsugunnan Yahudawa

Rahotanni daga yankin falasdinu sun bayyana cewa an yi taho mu gama tsakanin Sojojin Isra’ila da falasdinawa masu zanga-zangar nuna adawa da ci gaba da gina matsugunnan yahudawa a garin Beit dake kudancin Nablus a gabar yammacin kogin jodan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kungiyar Red Creasent ta fadi cewa sojojin Isra’ila sun jikkata wasu falasdinawa guda 7 bayan da suka harebesu da harsashin roba. yayin da wasu guda 30 kuma suke fama da matsalar Numfashi bayan da suka shaki hayaki mai sa hawaye da suka harba musu, cikin wadanda suka ji rauni har da wasu yan kasashen wajen dake goyon bayan falasdinawa.

A birnin Qudus sojojin Isra’ila sun yi amfani da karan bomb da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa falasdinawa a lokacin da riciki ya barke tsakaninsu a kabarin Al-yousefia da hakan ya jawo wasu falasdinawa guda 10 fuskantar matsalar numfashi,

Yanzu haka dai sama da yahudawa 600,000 ne ke zaune a rukunin gidaje 230 da aka gina tun a shekarata 1967 a yankunan falasdinawa da Isra’ila ta mamaye a gabar yammacin kogin Jodan da gabashin Qudus, kuma dukkan wadanan gine-ginen haramtattu ne bisa dokokin kasa da kasa, kuma kwamitin tsaro na MDD ta yayi tir da su a wasu kudurori da ya fitar.

342/