Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ya kuma yi kiran kara karfafa karfin sojin kasarsa, domin tunkarar abunda ya kira ‘’dakarun makiya’’.
A jawabin da ya yi jiya Litini, na zagayowar bikin cika shekaru 76 na jam’iyyar kwadago a kasar, Kim Jong-un, ya ce Amurka ce ummul’aba’in duk tashe tashen hankulan dake faruwa a yankin na koriya.
Yayin bikin koriya arewa ta nuna wasu sabbin makamai data samar, ya caccaki makwabciyar kasar, koriya ta Kudu da zama damo mai harshe biyu, inda yayin da take tir da makamman koriya ta Arewa, a daura guda kuma tana na ta.
Shugaban korioyar ta arewa, ya kara da cewa babu kamshin gaskia a kalamman gwamnatin shugaba Biden, na cewa ba ta da wata muguwar manufa ga kasarsa.
342/