Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : nakalto Mohammad Eslami shugaban hukumar makamashin nukliya ta kasar Iran ya na fadar haka wa kamfanin dillancin labaran Sputnic na kasar Rasha a birnin Moscow.
Eslami ya bayyana damuwarsa kan irin yadda hukumar IAEA take sukar shirin nukliyar kasar Iran duk da cewa tana kiyaye dukkan dokoki da sharuddan hukumar da kuma yarjejeniyar NPT.
Eslami ya ce jami’an hukumar IAEA su na sanya ido a kan ayyukan nukliyar kasar Iran ta hanyar na’urorin daukar hotuna ko kuma wani lokacin su zo da kansu don ganewa idanunsa yadda ayyukan suke tafiya.
Daga karshe shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran ya ce har yanzun Iran ta na tashe makamashin uranium ne gwagwadon bukatar ta.
342/