17 Satumba 2021 - 10:36
​Iran, Rasha, Cana Da Pakistan Sun Bukaci Gwamnatin Hadin Kan kasa A Afganistan

Ministocin harkokin waje na kasashen Iran, Rasha, Cana Da kuma Pakistan sun bukaci kungiyar Taliban wacce take iko da kasar Afganistan ta kafa gwamnatin hadin kan kasa wacce za ta sami wakilci daga dukkan dukkan kabilu da bangarorin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministocin guda hudu suna fadar haka a wani taron da suka gudanar a jiya Alhamis a birnin Dushambe babban birnin kasar Tajakistan, inda a halin yanzu ake gudanar da taron kasashen kungiyar SCO ko Shanghai Cooperation Organization.

Hossein Amir-Abdollahian, Sergei Lavrov, Wang Yi, and Shah Mahmood Qureshi duk sun jaddada bukatar hana ayyukan ta’addanci da kuma ci gaba da noman miyagun abubuwan sha masu lalata matasa.

Kungiyar Taliban ta kwace iko da kasar Afganistan a farkon watan da ya gabata, bayan da sojojin Amurka da kawayenta suka fice daga kasar babu shiri.

Taliban ta yi alkawalin kafa gwamnatin hadin kan kasa, amma ya zuwa yanzu dai ta kafa gwamnatin rikon kwarya wacce mafi yawan jami’anta ‘yan kungiyar ne.

342/