11 Satumba 2021 - 13:06
Goyon Bayan Shugaban Majalisar Malaman Afghanistan Kan Gwagwarmayar Panjshir

Shugaban Majalisar Malamai na dukkan lardunan Afganistan, yan mai goyon bayan gwagwarmayar ta mayakan Panjshir, ya jaddada cewa masu cin zarafi da yan kanzagi a Afghanistan sun zamo halakakku.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) –Abna,ya fitar majiyoyin labarai na Afghanistan sun bayar da rahoton goyon bayan shugaban Majalisar Malamai na larduna 34 na kasar don nuna adawa da gwamnatin Taliban.
Maulwi Habibullah Hussam, shugaban Majalisar Malamai na dukkan lardunan Afghanistan, ya goyi bayan tsayin daka na mayakan Panjshir tare da jaddada cewa masu kai hare -hare da masu cin zarafi a Afghanistan sun halaka.
Maulwi Habibullah ya jaddada: Panjshir za ta ci gaba da wanzuwa mai ƙarfi da wadata da nasarar Allah, amma masu cin zarafin sun tabbatar da lalacewar gwamnatin su tun kafin sanarwar membobin majalisar ministocin gwamnatin rikon kwarya din. Kasancewar su ‘yan amshin shata masu yada kabilancin kasa sun fallasa taken karyarsu na bin addinin Islama. 'Yan Taliban abin kyama ne ga Musulunci da Afghanistan.
A gefe guda kuma, Haj Ghausuddin Ghazat, daya daga cikin kwamandojin shekarun jihadin mutanen Afganistan kan sojojin mamaya na tsohuwar Tarayyar Soviet, ya shiga cikin dakarun gwagwarmaya na kasa kan gwamnatin Taliban a lardin Panjshir.
Haji Ghousuddin Ghazat ya tafi Panjshir bayan faduwar Mazarish-Sharif ga 'yan Taliban.

342/