4 Satumba 2021 - 08:32
​Lebanon: Wata Tawagar Gwamnatin Kasar Lebanon Za Ta Ziyarci Kasar Syriya, Jordan Da Kuma Masar Daga Yau Asabar

A yau Asabar ce ake saran wata tawaja ta gwamnatin kasar Lebanon wacce ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwaryan kasar zai jagoranta zata ziyarci kasashen Siriya da Jaorda da kuma Masar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta AL-Manar ta bayyana cewa wannan ita ce ziyara ta farko wacce jami’an gwamnatin kasar Lebanon za su ziyarci kasar Syriya fiye da shekaru 10 da suka gabata. Labarin ya kara da cewa tawagra wacce za ta gana da ministan harkokin wajen kasar Siriya Faisal Mikdad da kuma shugaba Bashhar Al-Asad za ta tattauna da su ne kan aikin jawo iskar gas daga kasar Masar da kuma wutan lantarki daga kasar Jordan zuwa Lebanon.

Wannan yana zuwa ne bayan da shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Sayyid Hassan nasarallah ya sayo jiragen ruwa na man fetur daga kasar Iran, kamar yadda yayi alkawari, zuwa kasar ta Lebanon don sawwakawa mutanen kasar mummunan halin karancin makamashin da kasar take fama da shi. Tuni dai jirgi na farko ya isa kasar Syriya ya na jiran a sauke shi zuwa kasar ta Lebanon.

342/