Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgediya Janar Mohammad Yusuf Khoshqalb mataimakin shugaban rundunar sojojin sama ta kasar ya na fadar haka, ya kuma kara da cewa sabon garkuwan makaman linzamin ya na da tsarin zamani na tsaron sama, kuma zai iya wargaza makamai masu linzami na makiya nau’i daban-daban a kuma wurare daban-daban.
Khosqalb ya kara da cewa, nan gaba kadan rundunarsa za ta fitar da wani nau’in garkuwan makaman masu linzami samfurin Mersad, amma wanda ya fi wannan sauri da kuma zuwa sama.
Sojojin kasar Iran dai suna aiki tukure don wadatar da sojojin kasar da makaman zamani da kuma garkuwar makamai daban daban a cikin shekarun da suka gabata. Wanda hakan ya sa sojojin kasar a halin yanzu sun wadatu da makamai na zamani da kuma masu inganci, kirar cikin gida.
342/