28 Agusta 2021 - 11:19
Turkiyya Na Nazarin Bukatar Taliban Na Tabbatar Da Tsaro A Filin Jirgin Saman Kabul

Kasar Turkiyya, ta ce tana nazari game da bukatar da kungiyar Taliban data kwace mulki a Afghanistan ta gabatar mata na tabbatar da tsaro a filin jirgin saman Kabul.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Turkiyya ta ce ta samu bukatar kungiyar Taliban a Afganistan ta gudanar da aiki da filin jirgin sama na kasa da kasa a Kabul, jim kadan bayan Ankara ta sauya shawarar samar da tsaro ga filin jirgin bisa umarnin Amurka saboda tabarbarewar yanayin tsaro a kasar. Da yake magana a wani taron manema labarai a Santambul ranar Juma'a, Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce,

“Taliban ta gabatar da bukata dangane da aikin tabatar da tsaron filin jirgin saman Kabul, Amma har yanzu ba mu yanke shawara ba. " Al’amuran tsaro dai sun tabarbare a filin jirgin saman na Kabul, inda ake ci gaba da aikin kwashe mutane, tun bayan jerin hare haren da sukayi sanadin mutuwar mutane sama da 100 ciki har da sojin Amurka 13, wanda kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa.

M. Erdogan ya yi Allah wadai da munanan hare -haren sannan ya jaddada cewa irin wadannan hare-haren na IS na nuna babbar barazanar da kungiyar ta’addanci ke yiwa yankin da ma duniya baki daya. Ya ce ya kamata a dawo da kwanciyar hankali a Kabul kafin Turkiyya ta yanke shawara game da filin jirgin sama saboda akwai barazana har yanzu.

342/