23 Agusta 2021 - 11:53
IRGC : Iran Za Ta Shigo Da Rigakafin Korona Ne Kawai Daga Kasashe Masu Aminci

Babban kwamandan Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC), ya ce Iran za ta shigo da rigakafin cutar korona ne kawai daga kasashen da tabbas alluransu ke da aminci, ko kuma za ta yi amfani da riga kafin da ta ke samarwa a cikin kasar

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Manjo Janar Hossein Salami, ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar wani taro kan yaki da cutar korona a lardin Kerman da ke kudu maso gabashin kasar a ranar Lahadi.

Salami ya ce, "Saboda rashin yarda, ba za mu iya amincewa da abokan gaba ba, kuma mu ba su damar sanya allurar rigakafin a jikin mutanen mu, saboda mun san cewa a cikin dabarun abokan gaba, komi zai iya faruwa musamman domin a lahanta ‘yan kasarmu’’ inji Manjo Janar Salami.

Ya kara da cewa ‘’ko takunkuman taltalin arzikin da aka kakabawa kasar wani yunkuri ne gurgunta al’ummar Iran’’.

342/