18 Agusta 2021 - 13:49
Iran Da Rasha Sun Canza Yawu Game Da Batun Komawa Tattaunawar Vienna

Kasashen Iran da Rasha, sun canza yawu game batun komawa tattaunawar Vienna da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Yayin wata ganawa manyan jami’an diflomatsiyan kasashen biyu kana wakilai a kungiyoyin kasa da kasa dake Vienna, Mikhaïl Oulianov na Rasha da Kazem Gharibabadi sun tattauna kan yiwiwar komawa tattaunawar da aka dakatar sakamakon shirye shiryen mika mulki ga sabuwar gwamnati a Iran.

Tun watan Afrilu ne wakilai daga kasashen da suka rage a yarjejeniyar ta 2015, bayan ficewar Amurka ke tattaunawa a Vienne da nufin sake dawo da Amurkar a cikin yarjejeniyar da kuma dagewa Iran jerin takunkuman da aka kakaba mata.

Tun lokacin bangarorin sun yi tattaunawa har guda shida a Vienna, wandanda bayyana samun ci gaba duk da cewa dai akwai sabanin da ake cin karo da shi.

342/