ABNA24 : Mai magana da yawun ƙungiyar ta Hamas Abdullateef Al-Кanu’iy ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da manema labarai inda ya ce lalle al’ummar Gaza ba za su ci gaba da haƙurin zama cikin irin wannan yanayi ba, lalle za su ci gaba da yin dukkanin abin da za su iya wajen kawo ƙarshen wannan killacewa.
Kakakin na Hamas ya ci gaba da cewa al’ummar Gazan ba za su bari nasarar da suka samu a kan Isra’ila a yaƙin baya-bayan nan da ta ƙaddamar kan Zirin ya tafi haka kawai ba, za su yi amfani da wannan damar wajen ƙwato haƙƙoƙinsu.
Tun dai bayan kawo ƙarshen wannan yaƙin da kuma nasarar da dakarun gwagwarmayar suka samu, haramtacciyar ƙasar Isra’ilan ta ƙara matsin lamba da kuma killace Zirin na Gaza da take yi ta sama da ƙasa da kuma ruwa lamarin da ke ci gaba da sanya al’ummar Gaza cikin mawuyacin hali.
342/