Kamfanin Dillancin Labarain ƙasa da ƙasa Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Rahoton ya ce, wadannan matakai na da nufin jawo kungiyar Hizbullah cikin rikici kai tsaye da kuma tilasta mata kare yankunanta da kuma wuraren zaman jama'a, matakin da ka iya fallasa wuraren kungiyar da kuma sanya ta shiga cikin hare-hare kai tsaye da kuma samun damar kai hare-hare daga sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Jaridar Al-Akhbar ta kasar Labanon ta bayyana cewa, a cikin 'yan makonnin da suka gabata an gudanar da tarurruka tsakanin jami'an Siriya da na Isra'ila da nufin tsarawa da kuma ingiza kungiyoyin masu dauke da makamai domin daukar mataki kan kasar Labanon.
Your Comment