Zanga-zangar da ma'aikatan kafar yada labarai suka yi a gidan talabijin na Aljazeera domin nuna adawa da kisan gillar da aka yi wa 'yan jarida biyu, Anas Sharif da Mohammed Qariqa, da Ibrahim Zahir da Mohammed Noufal, masu daukar hoto na kafar sadarwar.
Sannan an gudanar da zanga-zangar a Tunisia na yin Allah wadai da shahadar 'yan jarida 6 na Falasdinawa a Gaza
Dubban masu fafutuka na kasar Tunusiya sun gudanar da zanga-zangar nuna bacin rai a gaban gidan wasan kwaikwayo na birnin Tunis, inda suka yi Allah wadai da laifukan ta'addancin da gwamnatin sahyoniya ta yi wa 'yan jaridan Palastinawa a zirin Gaza.
An gudanar da gangamin ne bayan sanar da shahadar ‘yan jarida 6 na Falasdinawa – ciki har da ‘yan jaridar Aljazeera guda biyu, Anas Sharif da Mohammed Qariqa – bayan harin bam da aka kai a tantin su da ke kusa da asibitin Shifa da ke birnin Gaza.
Mahalarta taron sun yi ta rera taken nuna rashin amincewa da laifukan da gwamnatin sahyoniya ta aikata ta hanyar toshe muryar gaskiya a Gaza.
Masu zanga-zangar sun kuma dauki ci gaba da mamayewa da kakaba yunwa da gwamnatin sahyoniyawa ta ke yi wa al'ummar Gaza a matsayin babban laifi tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa don dakile wannan bala'in jin kai.
Bayan wannan harin ta'addancin ƙasashe da dama sun yi allawadai da harin tare da neman kawo karshen wannan ta'addanci.




Your Comment