Kamfanin Dillancin Labarain ƙasa da ƙasa Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Jaridar yahudawan sahyoniya ta Yedioth Ahronoth ta bayyana cewa shugabannin hukumar leken asiri ta gwamnatin Mossad da hukumar tsaron cikin gidanta Shin Bet sun nuna adawa da shirin mamaye birnin Gaza sakamakon tsoronsu da sakamakon hakan zai haifar.
Dangane da haka ne gidan talabijin na Sahayoniyya Channel 12 ya ruwaito cewa Tzachi Hangbi shugaban kwamitin tsaron Isra'ila ya nuna adawa da shirin Netanyahu na Gaza a wani taron majalisar ministocin kasar da aka gabatar.
Your Comment