25 Yuli 2021 - 17:18
​Jirgin Ruwan Yakin Iran Ya Isa St. Petersburg Don Halattar Atisayen Sojojin Ruwa Na Kasar Rasha

Jakdan kasar Iran a Mosco ya bada sanarwan cewa kataparen jirgin ruwan yaki na kasar Iran mai suna Sahan ya isa birnin St. Petersburg na kasar Rasha kwana guda kafin a fara atisayin sojojin ruwa na kasar ta Rasha karo na 325.

ABNA24 : Har’ila yau tare da jirgin akwai wani jirgin ruwan yakin na Iran shi ma, mai suna Makran yana tare da shi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa, a yau Lahadi ne za’a fara itisayin kuma jimillan jirage yaki na ruwa da zasu halarci wannan atisayin za su kai 54 da kuma sojojin ruwa 4000.

Kasashen India, Iran da Pakistan da wasu kasashe da dama ne zasu shiga atisayen.

Jalili ya kara da cewa babban kwamandan sojojin ruwa na kasar Iran Rear Admiral Hossein Khanzadi tuni ya isa kasar Rasha don halattan wannin atisayin. Kuma ana saran zai ga na da manyan manyan jami’an tsaron kasar ta Rasha da na wasu kasashe.

342/