ABNA24 : An tsara shugaba Ouatara zai gana da Mista Gbagbo, a ranar talata mai zuwa a fadar shugaban kasar.
Ana kallon wannan a matsayin manuniya ta cewa kasar ta kama hanyar kawo karshen rikita rikitar siyasa da kuma zurfafa batun hadin kan kasa.
Mista Gbagbo dai ya koma kasar ne bayan shafe shekaru goma yana tsare a kotun ICC, wacce ta yi masa shari’a kuma daga karshe ta wanke shi game da zargin cin zarafin bil adama.
Idan dai ganawar ta ranar Talata ta tabbata ita ce karon farko ta tsakanin Alassane Ouattara da Laurent Gbagbo, tun bayan mummunan rikicin da ya biyo bayan zaben shugabancin kasar na tsakanin shekarar 2010-2011.
Rikicin na waccen lokacin ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 3,000 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
342/